← Back to all albums

General · Photo Album

JIGAWA STATE HISBAH PARADE 2026

BIKIN YAYE DAKARUN JIGAWA STATE HISBAH 2,600 An gudanar da bikin yaye dakarun Jigawa State Hisbah guda 2,600 da suka kammala horo a sansanin NYSC Camp, Fanisau, Dutse, Jihar Jigawa. Bikin ya gudana cikin nasara da lumana, inda dakarun suka samu horo da shawarwari da suka dace domin kara inganta aikinsu na tabbatar da zaman lafiya, tsari da kyautata rayuwar al’umma. An samu halartar manyan jami’an gwamnatin Jihar Jigawa, karkashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Dr. Umar Namadi, FCA, tare da Mataimakin Gwamna, Sakataren Gwamnati na Jiha (SSG) da sauran manyan jami’an gwamnati, shugabannin hukumomi, malamai da sauran manyan baki. An gudanar da bikin cikin tsari da kwanciyar hankali, kuma an yi lafiya an tashi lafiya. Muna taya sabbin dakarun murnar kammala wannan muhimmin mataki, tare da fatan za su yi amfani da ilimi da horon da suka samu wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya, ladabi da kishin kasa.

1 photographs in this album